NAHCON za ta rage kudin tafiya aikin Hajji

0
6

  NAHCON za ta rage kudin tafiya aikin Hajji

Hukumar lura da aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ta bayyana cewa akwai yiwuwar za ta rage kudin aikin Hajji. 

Sabon Shugaban hukumar, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ne ya bayyana hakan a ranar da ya karbi tawogar kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dattijai ta kasa. 

Hakan bai sanya kowa cikin shakku game da manufar sa ba wanda yake tsammanin barin wani abin tabbataccen alama kamar ta shugabanni biyu da suka gabata. 
Da yake gabatar da jawabin nasa, Alhaji Hassan yayin da yake tabbatar da sauraron rahoton kwamitin harkokin waje na Majalisar Dattawan, ya bayyana cewa babban abin da ya fi mayar da hankali idan aka tabbatar da shi a matsayin shugaba shine rage kudin aikin Hajji. 
Ya bayyana cewa zai yi iya kokarin sa ya ga an sanya kudin ya zamto mafi araha da wadata ga mafi yawan al’ummar musulmi. 
Barista Hassan kuma jaddada wannan kudiri nasa a cikin jawabin sa yayin bikin karbar shugabanci daga hannun wanda ya gada, Barista Abdullahi Mukhtar Muhammad.
Ya kara da cewa shugabancin sa zai bada karfi sosai wajen daidaita aikin Hajjin tun daga wannan shekarar.
“Mun fahimci cewa lokacin da sauye-sauye suka canza, haka nan dole ne muma number canja. Dole ne mu zage dantse mu tunkari wannan sabon kalubalen da ke gaban mu.
” Don haka tilas ne mu kara kawo sabbin dabaru na aikin Hajji da kuma rage farashin aikin Hajji ta yadda za mu iya karfafa tare da baiwa galibin musulmai masu aminci damar gudanar da wajibcin da Allah Ya umarta da kuma amsa kiran sa. 
“Tabbas yana da matukar mahimmanci a gare mu mu bi wannan hanyar duk da cewa aiki ne ja a gaban mu, amma da yardar Allah za mu cimma nasara,” Barista Hassan ya ce

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here