SADAUKARWA
Covid-19: NAHCON tabi umarnin Saudiyya na dakatar da Umrah na wucingadi
Hukumar kula da harkokin Hajji ta kasa (NAHCON) ta jawo hankalin maniyyata daga Najeriya zuwa Saudi Arabia don Umrah ko zuwa masallacin Manzon Allah a Madinah da su dakatar da shirin har zuwa wani lokaci.
Kiran ya zo ne biyo bayan dakatar da Umrah da gwamnatin Saudi Arabiya ta yi a matsayin matakin kariya daga yaduwar cutar Coronavirus, wacce ake wa lakabi da COVID-19.
Wannan sanarwar na kunshe ne a takardar sanarwa da Shugaban NAHCON, Alhaji Zikrullah Olakunle Hassan ya fitar ran alhamis ta hannun Fatima Sanda Usara, Shugabar Fannin Hurda da Jama’a na hukumar.
Sanarwar ta ce rahotanni sun baiyana cewa, kawo yanzu, cutar ta bazu zuwa kasashe 48 a duniya tare da kama a kalla mutane 82,164 a rahoton da ya fito na ranar 27 Febrairu 2020.
Dadindadawa kuma, COVID-19 ta janyo asarar rayuka da yawa a wasu kasashen, lamarin da ya tilasta musu bada umarnin rufe makarantu da sauran guraren taron jama’a.
Abin farin ciki ne, inji takardar sanarwar, a fahimci cewa Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kasa, wata hukuma a karkashin Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, kamar yadda a yau Alhamis, 27 Febrairu, 2020 ta ba da rahoton cewa babu wani rahoton COVID-19 a Najeriya.
“Ma’aikatar lafiya ta tarayya ta dauki dukkan matakan da suka dace don dakile cutar a Najeriya”, in ji takardar bayanin.
Saboda haka, NAHCON tayi maraba da wannan matakin karfafa gwiwa da Saudi Arabiya ta bayar kuma tana mai tabbatar da jajircewarta da bada hadin kai a kan duk wani mataki na kare lafiya da rayukan musulman duniya, da ma al’umma baki daya.
“An dauki wannan matakin ne daidai da ka’idojin kasa da kasa da aka amince da su kan rage yaduwar cutar,” in ji sanarwar.
A sakamakon haka, NAHCON tana gargadi ga maniyyata aikin Umrah daga Najeriya da su lura cewa wannan dakatardar tana da tasiri ga wadanda tuni an ba su takardar izinin tafiya da kuma wadanda za su fara shirin tafiya da wadanda ke shirin yin hakan a nan gaba.
NAHCON ta bukaci duk masu ruwa da tsaki da su bi umarnin kuma su jira ƙarin bayani daga hukumomin Masarautar Saudiyyar
Saudiyya ta fara sanya sababbin silin a Masallacin Harami
A wani mataki na ci gaba da fadadawa, Babban Shugaban kula da masallatan Harami guda biyu na Saudi Arabia ya bada umarnin fara sanya sababbin silin masu ado a saman rufin ginaginen Harami da kewayen Mata