Na cimma manufofi 17 lokacin da nake shugabancin NAHCON- Barr. Abdullahi Mukhtar

0
264

Barr Abdullahi Mukhtar


Shugaban hukumar ta NAHCON mai barin gado, Barista Abdullahi Mukhtar Mohammed ya ce lokacin da yana shugabancin hukumar, ya cimma manufofi guda 17 da nufin kawo sauyi a harkar gudanar da aikin hajji a Nijeriya.
Barista Mukhtar ya baiyana hakan ne lokacin da yake mika ragamar shugabanci ga sabon shugaban hukumar, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan a Abuja. 
Tsohon shugaban ya godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa yadda ya bashi damar aikin jagorantar hukumar tare da tawagarsa.
“Babu wani abu na dindindin. Na yi farin ciki cewa wadanda za su yi nasarar aikin Hajji sun kasance daga da’irar wadanda suka san aikin Hajji.
“Muna da hangen nesa kan yadda cibiyar aikin Hajji zata kasance mai samar da kudaden shiga ga hukumar. 
“Don haka, waɗannan ayyukan sun isa ga hukumar don sarrafa kanta da aiwatar da aikin hajjin,” Barista Mukhtar ya fada

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here