Hajj Reporters Ta Bude Jaridar Yanar Gizo-gizo Ta Hausa, Tana Kuma Shirin Bude Manhajojin Telebijin Da Rediyo

0
248



Independent Hajj Reporters, kungiya mai zaman kan ta da ta ke sa ido da kuma kawo rahotanni a kan aikin Hajji a Nigeria da kasar Saudi Arabia, kuma ta ke wallafa mujallar Hajj Reporters da kuma kafar Hajj Reporters ta yanar gizo-gizo, na sanar da bude jaridar yanar gizo-gizo ta harshen Hausa, mai suna @hajjreportershausa.com
Haka kuma, kungiyar ta budewa jaridar hausan dandalin shafukan sadarwa da suka hada da; @facebook.com/hajjreportershausa da kuma twitter @HajjReportershausa.
Kungiyar ta sanar da bude jaridar hausan ne ranar Talata, a takardar sanarwar da ta fitar, mai dauke da sa hannun shugaban ta na kasa, Ibrahim Muhammad. 
Sanarwar ta ce “samar da shafin hausan na yanar gizo-gizo na Hajj Reporters ya zo ne sakamakon kiraye-kiraye da dumbin jama’a su ka rika yi na samar da wata sahihiyar kafa da za ta rika ilimantar da wayar musu da kai a kan aikin Hajji da Umrah a yaren su na gado.”
Sanarwar ta kara da cewa Hajj reporters.com da mujallar Hajj Reporters, wato IHR, tana aika sakon kar ta kwana ta wayoyin dumbin al’umma domin wayar da kai. 
Ta kuma bayyana cewa tuni shirye-shirye sun yi nisa domin samar da Manhajojin Hajj Reporters telebijin da rediyo na yanar gizo-gizo, da kuma samar da gangariyar kafar bincike ta yanar gizo-gizo, wacce za ta rika bawa al’umma damar shiga su samu muhimmai kuma sahihan bayanai da aka tace su bayan zuzzurfan bincike a kan Hajji da Umrah daga ko ina a fadin duniya. 
Kungiyar ta kara da cewa “ita wannan sabuwar jaridar hausan ta Hajj Reporters za ta maida hankali ne a kan ilimantar da wayar da kan maniyyata a kan Hajji da Umrah, abubuwan da a ke so maniyyaci ya yi da kuma wanda ba a so, labaran gida da na kasashen waje a kan Hajji da Umrah, da kuma wayar musu da kai a kan kiyaye dokokin kasa na Nigeria da kuma Saudi Arabia. 
“Mun yi ittifakin cewa babbar matsala wajen ilimantar da wayar da kan mahajjata ita ce ta hanyar isar musu da sakon ta yadda za su fahimta har su aiwatar da abinda aka koya musu a aikace a lokacin aikin hajji. 
” Sabo da haka, IHR ta dauki gabaran mu’mala da mahajjata ta yin amfani da yaren da su ka fi sabawa da shi,” inji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here