An Karrama Tsohon Shugaban NAHCON A Masarautar Zazzau

0
242

dAGA Mustapha adamu 

An karrama shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) mai barin gado, Barista Abdullahi Mukhtar Muhammad a Zaria ranar Lahadin da ta gabata. 

Hakanan Zaka Iya Karatu: Kasashe 23 sun Amfana daga Wurin Yin Amfani da Hady & Adahi – Ma’aikatar aikin Hajji ta Saudiyya 

Barista Muhammad, ya samu wannan lambar yabo ne daga makarantar Tazkiya Qur’anic dake garin Zaria, a karkashin masarautar Zazzau.

Da yake gabatar da jawabin sa a yayin taron karramawar, shugaban makarantar ta Tazkiya Qur’anic, Ibrahim Ahmad Maqary, ya ce makarantar ta baiwa tsohon shugaban wannan lambar yabo ne sakamakon irin gagarumar gudummawar da ya bayar wajen cigaban hukumar aikin hajji ta kasa da addinin musulunci a jihar Kaduna baki daya.

“lambar girmamawa ta jagoran hidamtawa addini ta wannan shekara mun miqata ga Barista Abdullahi bisa jajircewar sa wajen ciyar da addinin musulunci da musulmai baki daya gaba a wannan kasa baki daya” inji shugaban.‎
Shima da ya ke tofa albarkacin bakin sa a yayin taron, Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir Ahmad EL Rufai, ya yabawa tsohon shugaban tareda kira ga al’umma da suyi koyi da ire-iren wadannan kyawawan dabi’o’i nasa domin ciyar da kasa da musulunci gaba baki daya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here