Mun tanadi sababbin manyan jirage 3 don jigilar aikin Hajjin bana- Azman

0
5

Daga Mustapha Adamu
Kamfanin sufurin jiragen sama na Azman ya bayyana cewa ya kammala dukkan shirye-shirye tsaf domin tunkarar aikin Hajjin 2020.
Yayin da ya ke jawabi lokacin da ya karbi bakuncin ya’n kungiyar ya’n jarida masu rahoton aikin Hajji ta Kano, wadan da su ka kai ziyara a babban ofishin Azman din da ke birnin Kano ran litinin, Jami’in kula da bayanai na kamfanin, Muhammad Hadi Abdulmunaf ya bayyana cewa ya sayo sababbin manyan jirage guda biyu masu lambar kira A340-600. 
Abdulmunaf ya ce kamfanin zai yi amfani da sababbin jiragen, masu cin fasinjoji 410 ne wajen yin cikakken aikin jigilar alhazai cikin inganci da kwanciyar hankali a Hajji mai zuwa. 
Ya kuma yi bayanin cewa tuni aka kawo daya daga cikin jiragen zuwa Nigeria a watan jiya, shi kuma dayan zai iso kasar nan a watan da muke ciki. 
Jami’in ya kara da cewa kamfanin ya tanadi wani jirgin na kar ta kwana, irin wadannan jirage biyun domin ganin ya kammala jigilar alhazan ba tare da wata matsala ba. 
“Ai shirin da muke na jigilar aikin Hajjin bana kusan a kammale ya ke. Maganar nan da na ke yi da ku, mun sayo manyan jirage guda biyu masu lambar kira ta A340-600 kuma suna cin fasinjoji 410.
“Daya ma har ya riga ya zo, dayan kuma muna sa ran a watan nan da muke ciki zai karaso. Muna kuma da wani irin su mun tanade shi a matsayin na ko ta kwana sabo da ba ma son mu samu matsala. 
” Mun yi jigilar aikin Hajji bara. A bana kuma mun yi nazari a kan irin kura-kuran da muka yi kuma har mun yi gyare-gyaren matsalolin,” jami’in ya ce. 
Abdulmunaf ya kara da cewa jiragen na da wajen zuba kaya mafi girma a jiragen da za su yi jigilar aikin, ya kuma tabbatarwa mahajjata cewa zasu sauka ne tare da kayan su babu jeka ka dawo. 
Ya kuma bayyana cewa kamfanin na tataunawa a kullum da hukumar kula da aikin hajji ta kasa (NAHCON) domin ganin cewa ya yi aiki a bisa bin doka da tsarin da hukumar ta tanada. 
Ya tabbatar da cewa Azman za ta yi ai a kan doron dokoki da ka’idojin da NAHCON ta tanada. 
Ya kuma tabbatar da aniyar sa ta yin aiki hannu da hannu da ya’n kungiyar ya’n jaridar masu rahoton aikin Hajji a jhar a matsayin abokan tafiya domin a cimma manufar da aka sa a gaba. 
Da ya ke jawabin sa tun a farko, shugaban kungiyar na rikon kwarya, Nura Ahmad Dakata ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin karfafa zumunci da Azman domin su bada ta su gudunmawar wajen kokarin da a ke na ciyar da jigilar aikin Hajji gaba. 
Shugaban kuma ya tabbatar da yin rahotanni na gaskiya a kan kamfanin da kuma jigilar aikin Haji baki daya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here