COVID-19: NAHCON ta yi kira ga maniyyata Umrah da su je kamfanunuwan da su ka biya Umrah su karbi kudaden su

0
421
Kaaba

Daga Mustapha Adamu

Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ta yi kira ga maniyyata Umrah wadan da su ka biya ta kamfanunuwan sufurin jirgin sama masu lasisi da su tuntube su a kan su dawo musu da kudaden su.

Kiran ya zo ne bayan da Saudi Arabia ta dakatar da yin Umrah din sakamakon barkewar cutar COVID-19, wacce a ka fi sani da Coronavirus.

Sanarwar da NAHCON din ta fitar ranar Alhamis, mai dauke da sa hannun Shugabar sashen hurda da jama’a ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta yi kira ga maniyyatan da suka biya ta kamfanunuwan sufurin jirgin sama masu lasisi da su rika tuntubar su a kan kudaden na su idan Gwamnatin Saudiyya ta saki kudaden.

NAHCON ta kuma yi kira ga wadanda suka fuskanci matsala wajen karbar kidaden nasu da su kai korafi wajen jami’in aikace-aikace, ta hannun shugaban sashen dubawa databbatar da bin ka’ida, a layin Zakariyya Maimalari, Hajj House, Abuja, ko kuma a je kafa da kafa zuwa hukumar.

Sanarwar ta ce “duk wani korafi ya zamana an yi shi da  takardun shaida da kuma shaidar biyan kudi ga kamfanin,” sanarwar ta fada.

Sanarwar ta kuma nanatawa maniyyatan da su tabbatar sun biya kudaden su kai tsaye zuwa ga Kamfanunuwan sufurin jirgin sama masu rijista da hukumar ko kuma makamancin haka domin samun kudaden cikin sauki.

“Haka kuma hukumar na shawartar maniyyata aikin Umrah ko Hajji da suka biya ta kamfanunuwa masu zaman kan su da su tabbatar sun rubuta yarjejeniya a kan ko wanne irin tsarin da suka biya. A tabbata tsarin ya nuna irin hidimar da maniyyaci ya zaba tare da tabbatar da cewa yarjejeniyar ta kunshi sharuda.

NAHCON hukuma ce da ke da tsayawa tsayin daka don kare hakkin abokan hurdar ta da suka hada mahajjata da kuma kamfanunuwan sufurin masu zaman kan su,”

Domin karin bayani, a tuntubi Sashin dubawa da tabbatar  da bin ka’ida na NAHCON a kan wannan lambar-  08033826429.

Sai kuma sashin Visa da Consular na, NAHCON a kan- 07033701605.

Sanarwar ta tuna cewa a kwanan nan Ma’aikatar kula da Hajji da Umrah ta fitar da sanarwar, in da ta ke sanar da al’umma kan aniyar ta ta dawo da kudaden biza ta Umrah da maniyyata su ka biya.

Kiran ya zo ne bayan da Saudi Arabia ta dakatar da yin Umrah din sakamakon barkewar cutar COVID-19, wacce a ka fi sani da Coronavirus domin dakile yaduwar cutar a kasar.

Sanarwar ta bayyana cewa an tanadi na’ura da za ta yi aikin dawo da kudaden na Umrah da biza ga maniyyata ta hannun kamfanunuwan sufurin jirgin saman da suka biya.

Sabida haka tana kira ga maniyyata da suka biya ta sahihiyar hanya da su Je gurin kamfanunuwan da suka biya su karbi kudaden su

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here