Hajj 2020: Hukumar kula da walwalar alhazai ta Kano za ta fara horas da maniyyata

0
275
KANO FIRTS FLIGHT

Daga Mustapha Adamu

Hukumar kula da jin dadi da walwalar alhazai ta Jihar Kano ta bayyana cewa za ta fara kashin farko na ilimantarwa da horas da maniyyatan aikin Hajjin 2020 ranar Asabar, 7 ga watan Maris. 

Shugaban hukumar, Alhaji Muhammad Abba Dambatta ne ya bayyana hakan a ganawar da ya yi da manema labarai a ofishin sa, ranar Litinin. 

Alhaji Dambatta ya ce an tsara horaswar ne don wayar da kai da ilimantar da maniyyatan a kan abubuwan da ya kamata su yi a yayin aikin Hajjin a kasa mai tsarki. 

“Horaswar na daya daga cikin shirye-shirye da hukumar ta tsara domin ganin cewa maniyyata aikin Hajjin sun san abubuwan da su ka kamata su yi, da wadan da ba su kamata ba a kasa mai tsarki, a yayin aikin Hajji,” ya ce. 

Ya kuma kara da cewa an tsara shirin ne da niyyar wayar da kan maniyyata a kan sanin dokokin Kasar Saudiyya, gami da abin da ya kamata su yi da wanda bai kamata ba a kasa mai tsarki. 

Alhaji Dambatta kara da cewa hukumar ta dauki wasu malaman addinin musulunci da za su yi horon, wanda za a yi shi cikin wata daya. 

Dadindadawa kuma,  ya ce wasu jami’an hukumar da masu ruwa da tsaki za su kaddamar da makaloli a yayin horon a kan wasu abubuwan masu amfani ga maniyyatan. 

Ya kuma yi kira ga maniyyatan da su jajirce su rika halartar wajen horon. 

Ya kuma bayyana cewa tuni hukumar ta fara karbar Naira Miliyan 1.2 a matsayin kudin ajiya daga maniyyatan. 

Ya yi bayanin cewa duk da hukumar kula da aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ta bawa hukimomin kula da aikin Hajji na jahohi umarnin su karbi Naira Miliyan 1.5 a matsayin kudin ajiya, amma sabida wasu dalilai shi yasa hukumar tasa ta tsaya a kan Naira Miliyan 1.2 din. 

Ya ce ana tsammanin kowanne duk maniyyacin da ya fara biyan Naira Miliyan 1.2 ba zai ji kyashin cika ragowar kudin aikin Hajjin ba. 

“Kamar yadda ta faru a bara, kudin aikin Hajjin bai zarta Naira Miliyan 1.4 ba. Shi ya sa duk wanda ya biya Naira Miliyan 1.2 ba zai sha wahalar cika sauran ba idan hukumar kula da aikin Hajji,” ya ce. 

Shugaban hukumar ya ce da zarar maniyyata aikin Hajji sun biya kudin ajiya, hukumar za ta yi musu rijista domin fara gudanar da sauran cike- ciken takardu kafin su biya cikon kudaden

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here