An killace yankin jikin Ka’aba na wucin gadi domin feshin magani

0
345
briefly kaba empty

Yankin jikin Ka’aba, waje mafi tsarki a Musulunci ya kasance ba kowa tun safiyar Alhamis yayin da ma’aikatan lafiya su ke tsaftace harabar sakamakon bullar cutar coronavirus, kamar yadda hotuna da fayafayen bidiyo suka nuna.

Yankin, wanda a ka fi sani da Mataf a yaren larabci shine budadden wajen nan mai farin kasa da ya kewaye Ka’aba inda Alhazan da su ke ibadar Hajji da Umrah su ke yin dawafi.

Zagaye Ka’aba din na cikin rukunin yin aikin Hajji da Umrah da kowanne Alhaji sai ya yi, inda ake kewaye dakin ta yadda agogo ya ke kewayawa har sau bakwai. Haka kuma Saudi Arabia ta tsawaita dakatarwar da ta yi wa maniyyata ya’n kasashen waje da ma mazauna kasar ta hana su shigowa biranen Makkah da Madina yayin da fargabar yaduwar sabuwar cutar ta coronavirus ke karuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here