An yabawa Independent Hajj Reporters kan samar da kafar labarai ta Hausa

0
226

Daga Jabiru A Hassan, Kano. Maniyyata zuwa aikin Hajji da Umrah da sauran masu ruwa da tsaki kan Hajji da umrah a jihar kano ,sun bayyana jin dadin su bisa yadda kungiyar masu rubuta labarai da rahotanni ta “Independent Hajj Reporters” (IHR) ta kirkiro sabuwar hangar yada labarai da wayar da kai kan aikin Hajji da Umrah cikin harshen Hausa. Sannan sun nunar da cewa ko shakka babu wannan kafar sadarwa tazo daidai lokacin da make bukatar ta musamman ganin cewa mafiya yawan maniyyata dake fitowa daga yankunan karkara basu jin wani harshen sai Hausa wanda hakan abin a yaba ne kwarai da gaske. Malam Ahmad Lawan Abdullahi, Wanda kuma yake cikin kungiyar masu taimakon Alhazai a kano tun shekaru fiye da 30, yace ” kirkiro hanyar bada rahotannin aikin Hajji da Umrah abu ne da zai samarda wayewa da sanin halin da maniyyata suke ciki, tareda basu basu dama wajen bayyana ra’ayoyin su da yadda masu ruwa da tsaki suke yi masu hidimomi tun daga gida Nijeriya zuwa kasa mai tsarki”.inji shi. Shima a nasa tsokacin mamba a kwamitin kula da aikin Hajji a jihar Kano Alhaji Musa Haruna yace sun ji dadin kirkirar kafar bada labarai da rahotanni kan aikin Hajji da Umrah cikin harshen Hausa, tareda jaddada cewa za’a sami Karin dama ta jin halin da maniyyata suke ciki run daga fara shirin tafiya kasa mai tsarki da kuma yadda hukumomin kula da aikin Hajji na jihohi da ta kasa baki daya suke sauke nauyin da aka dora masu na tafiyar da aikin Hajji da Umrah cikin nasara. Tuni dai wannan sabuwar kafar yada labarai kan aikin Hajji da Umrah ta fara aikin ta wanda al’uma suke murna da kirkirar ta, sannan wasu suna bayyna fatan su na gaggauta Samar da kafar radiyo da talabijin domin kara bunkasa aiyuka da wayar da kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here