Covid-19: Gwamnatin Saudiyya ta damu da rayuwar ya’n kasar ta- Sheikh Dossary

0
5

Daga Mustapha Adamu Limamin masallacin Harami da ke birnin Makkah a kasar Saudi Arabia, Sheikh Dossary ya ce matakan dakile yaduwar cutar Covid-19, wacce a ka fi sani da coronavirus da gwamnatin kasar ke yi ya nuna cewa ta damu da rayuwar ya’n kasar. A yayin da yake hudubar Juma’a a Masallacin Harami na Makkah, a yau, Sheikh Dossary ya ce matakan da kasar ta ke dauka domin dakile yaduwar cutar ba wani bakon abu bane. Ya kara da cewa, duk wata kasa da ta damu da kiyaye lafiyar ya’n kasa da ma baki ma su zuwa to abar a jinjina mata ne a kuma taimaka mata da addu’o’i na alheri. Sheikh Dossary ya kuma yi kira ga al’ummar duniya da su ji tsoron Allah, tsoro na hakika, ya kara da cewa “duk wanda Ya ji tsoron Allah, to Allah Ya isar masa kuma zai azurta shi Ya kuma kare shi ta hanyar da bai taba tsammani ba.” Sheikh Dossary ya kara yin kira ga al’ummar Muslimi da su koma ga Allah su kuma dage da yawaita istigifari, ya kara cewa, hakan ne zai farantawa Allah har ma Ya ji kan al’ummar Ya kuma yaye wadan nan masifu da suke kunno kai. Ya kuma roki Allah da Ya yayewa al’umma wannan cuta ta coronavirus da kuma sauran cututtuka masu yaduwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here