Daga Mustapha Adamu Gwamnatin Saudi Arabia ta bada umarnin sake bude Masallatan harami na Makka da Madina, bayan rufe su na wucin gadi domin a yi feshin magani don dakile yaduwar cutar coronavirus, kamar yadda gidan telebijin na kasa TV Al Ekhbariyya ta rawaito. Saudi Arabia ta rufe wajajen bautar ne mafi tsarki a musulunci sabida bakin alhazai da masu yawon bude ido daga wasu kasashe 25 domin dakile yaduwar kwayoyin cutar. Ta kuma kara da cewa ya’n kasa da kuma mazauna yankin kasashen larabawa da suke son shiga Masallatan sai sun yi jira na kwanaki 14 bayan sun dawo daga wajen yankin. A halin yanzu dai Saudi Arabia ta sanar da bullar cutar a kan mutane 5 a kasar. Babu tabbaci daga rahoton Al Ekhbariyya ko za a bar alhazai su dawo yankin masallatan a kwana kusa