Labari da Dumi-duminsa: Wanda zai je Makka a Keke daga Jos har ya iso Daura

0
270

A labarin da Katsina Daily Post News ke samu yanzun nan da duminsa na nuna Aliyu Obobo matashin da ya hawo yar kwamarsa tun daga garin Jos zuwa Makka domin sauke faralin bana har ya iso garin Daura tashar Yamma Sai dai abin da ba mu da tabbas a kansa shi ne zai kwana a Daurar ko zai wuce zuwa kasa mai tsarki a cikin wannan daren. Wata majiyar ta rawaito mana cewa a nan cikin Daurar zai yi sallar Jumu’a sannan kuma ya je fadar mai Martaba Sarkin Daura ya yi gaisuwa kana daga karshe sai yan gari su yi masa rakiyar bankwana zuwa bakin gari

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here