Kalmar Hajji a harshen Larabci tana nufin nufi. Amma a shari’a tana nufin bautar Allah da yin wasu ibadu na musamman da suka zo a sunnar Annabi (SAW). kalmar “Umra” kuwa tana nufin ziyara.
Hukuncin aikin Hajji: Wajibi ne a kan dukkan mukallafi, saboda fadin Ubangiji (SWT) “Umarni ne daga Allah a kan mutane hajjantar daki mai alfarma ga duk wanda ya samu ikon tafarki a gare shi” (Al imran: 97).
Aikin Hajji rukuni daga cikin rukanan Musulunci guda biyar, kamar yadda ya zo a cikin Hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito.
“بني الإسلام على خمس شهادة أن لا إلـه إلا الله وأن محمدا رسول الله وإقام الصلوة وإيتاء الزكاة وحج البيت وصوم رمضان” رواه البخاري ومسلم.
“An gina Musulunci a bisa abubuwa guda biyar; shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah ne, da tsai da Salla da ba da Zakka da ziyartar Dakin Allah (Aikin Hajji) da azumtar watan Ramadan”
(Bukhari da Muslim).