Hajjin 2020: Karancin Fasfo Na Kawo Tsaiko Wajen Rajistar Maniyyata- IHR

0
219
Daga Jabiru Hassan
Kungiyar Masu Bada Rahotannin Aikin Hajji Da Umara (IHR) ta koka dangane da yadda karancin takardar buga fasfo ke kawo tsaiko wajen yiwa maniyyata rajista, inda hakan ke kawo matsaloli wajen tafiyar da aikin Hajjin wannan shekara ta 2020.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, mai dauke da sa hannun shugaban ta na kasa, Malam Ibrahim Mohammed, kungiyar ta yi bayanin cewa samar da isassun Fasfuna ga alhazai zai taimaka wajen yin rajista cikin sauri sannan mafiya yawan matsalolin da a ke gamuwa da su za su ragu kamar yadda a ke tunani.
Sanarwar ta ce samar da Fasfo mai shafuka 35 mai kuma wa’adin kwanaki 5 zai kasance abu mafi dacewa, kana kowane maniyyaci zai zamo cikin shiri da natsuwa bisa samun tabbacin tafiya kasa mai tsarki batare da samun tsaiko ba.
A karshe, IHR ta yi fatan cewa hukumar kula da shige da fice (NIS) za ta duba wannan matsala domin tabbatar da cewa komai yana tafiya yadda ake bukata

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here