Hajjin 2020: Kungiya mai zaman kan ta ta koka kan karancin takardar buga fasfo

0
6

Independent Hajj Reporters, kungiya mai zaman kan ta da ta ke kawo rahotanni kan al’amuran Hajji da Umara ta yi kira ga hukumar shige da fice ta kasa da ta tabbatar da yawaitar fasfo da ake yi ta yanar gizo, musamman mai shafi 32 mai kuma wa’adin shekaru 5 (na manya da yara) domin maniyyata aikin Hajjin 2020.
IHR a sanarwar da ta fitar ranar Litinin a Abuja, mai dauke da sa hannun shugaban ta na kasa, Ibrahim Mohammed ta yi takaicin cewa karancin fasfo din na kawo tsaiko wajen yin rijistar aikin Hajji da maniyyata suke yi a Najeriya. 
“Rahotannin da mu ke samu daga ya’n kungiyar mu, musamman wadanda suke jihohin Kaduna, Yobe da Kebab sun nuna cewa yawancin maniyyata da su ka je za a yi musu fasfo din, an fada musu cewa babu takardar buga fasfo din, inda sai dai a dauki bayanan su ta na’ura mai kwakwalwa sannan a ce su jira. 
“Kawo yanzu, yawancin maniyyatan da a ka dauki bayanan su karbi fasfo din na su ba,” sanarwar ta ce. 
Kungiyar ta yi nuni da cewa muhimmamcin samun fasfo da wuri ga maniyyata zai yi matukar amfani ga Hajjin 2020 kuma ya kamata ya zama babban abin kula ga duk wasu ma su ruwa da tsaki a kan aikin Hajji a fadin kasar nan. 
“Rijistar maniyyata, tattara takardu da bayanan su, samar da biza da kuma harkar biyan kudade da wasu sauran takardun tafiye-tafiye na kan shafin fasfo din na yanar gizo. 
Misali, bayanan sharuddan rijistar aikin Hajjin 2020 da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta fitar ya sanya faso ya zama matakin farko na yiwa maniyyaci rijista. 
“Sashi na 3.2, karamin sashi (iii) a karkashin shirin yiwa maniyyata rijista ya yi bayanin cewa”dole maniyyaci ya gabatar da kan sa da sahihan takardun tafiye-tafiye, sannan karamin sashi na 9  ya fito karara ya ce dole ne maniyyaci “ya mallaki sahihin fasfo na yanar gizo mai dauke da a kalla wa’adin watanni 6 daga ranar da zai tashi zuwa kasar Saudi Arabia,”
Sabo da haka mu na kira ga hukumar shige da fice ta kasa da sauran hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki da su gaggauta yawaitar wannan muhimmiyar takardar tafiye-tafiyen domin maniyyata aikin Hajji na 2020.
Rahotannin da IHR ta samu sun yi nuni da cewa rashin takardar buga fasfo din na kashe gwiwar wasu maniyyatan, musamman na karkara musamman yadda suke shan wahalar jigila zuwa ofishin hukumar shige da fice ta kasa domin a yi musu fasfo din. 
Sanarwar ta kara da cewa “aikin Hajji abu ne da ya ke son shiri tun da wuri a kan shirye-shiryen farko kafin na Hajji, musamman ma takardun tafiye-tafiyen kasashen waje na maniyyata domin ba wa maniyyata dama a dauki bayanan su wajen jigilar su zuwa kasa mai tssarki da sauran harkokin tafiya. 
Sa hannu
Independent Hajj Reporters
9 ga watan maris, 2020

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here