Hukuma kula da jin dadin alhazai ta Jihar Katsina na ci gaba da karbar kudaden ajiya wanda ta fara tun watan nuwambar 2019 har zuwa karshen watan Maris 2020

0
267

Hukumar kula da jin dadin alhazai ta Jihar Katsina na farin cikin sanar da maniyyata aikin Hajjin 2020 cewa hukumar na ci gaba da karbar kudaden ajiya wanda ta fara tun watan nuwambar 2019 har zuwa karshen watan Maris 2020.
Domin haka, hukumar na kara kira ga maniyyata zuwa sauke farali a wannan shekarar ta 2020, musamman wadan da ko asusun kudin ajiya basu bude ba da su hanzarta biya kafin karshen watan nan Maris. 
Ha kuma, hukumar na sanar da maniyyatan cewa za ta rufe karbar kudaden ajiya daga maniyyatan a karshen wannan wata na Maris a ofishin shiyoyin ta guda bakwai da ke fadin Jihar a Katsina, Mani, Dutsinma, Funtuwa, Kankiya, Daura da Malumfashi, kamar yadda hukumar kula da aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ta umarta. 
Daga karshe, hukumar ta kara jaddadawa dukkan maniyyatan da ba su samu damar biyan kudin kujera a ofishin ta na shiyoyi bayana rufewar ba da su tuntubi shelkwatar ta domin neman karin bayani. 
Allah Ya bada iko
SANARWA: BADARU BELLO KAROFI
JAMI’IN HULDA DA JAMA’A NA HUKUMAR KULA DA JIN DADIN ALHAZAI TA JIHAR KATSINA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here