Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Jihar Kano Na Ci Gaba Da Karbar Kudin Ajjiya Na Maniyyata

0
356

Daga Jabiru A. Hassan, Kano
Hukumar jin dadi da walwalar alhazai ta Jihar Kano ta bada sanarawar ci gaba da karbar kudin ajjiya na maniyyata maza da mata kamar yadda aka saba.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, hukumar ta jaddada aniyar ta dangane da tabbatar da yin shiri na ganin cewa an sami gagarumar nasara wajen gudanar da Hajjin bana.
Sanarwar mai dauke da sa hannun jami’ar Hulda da jama’a ta hukumar, Hajiya Hadiza Abbas Sanusi ta bayyana cewa ana ci gaba da karbar kudin ajjiya na naira miliyan daya da dubu Dari biyu (N1,200,000,000) daga maniyyata dake kananan hukummomi 44 na jihar ta Kano. 
A karshe, sanarwar ta yi kira ga maniyyata da su gaggauta bada wadannan kudade na ajjiya ta yadda hukumar alhazan za ta gudanar da shirye-shiryen ta duba da yadda ake samun sabanin dokoki daga hukumomin kasar Saudiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here