Ma’aikata 450 ne Za Su Rika Tsaftace Harami Sau 6 a Kowacce Rana

0
5

Yawan ma’aikatan da su ke tsaftace babban masallaci na birnin Makka, a kasa mai tsarki sun karu zuwa dari hudu da hamsin (450), ofishin shugaban kula da harkokin masallatai guda biyu masu tsarki ne ya bayyana hakan ranar Talata. 
Rahotannin da suka fara fitowa sun daga wani bangare na kafafen yada labarai sun bayyana cewa tawogar ma’aikatan tsaftar mai mambobi dari uku (300) ne ke aikin goge-goge, share-share da sanya waje yayi kamshi a yankin ka’aba wato Mataf da sauran gurare a cikin babban masallacin, Kamfanin yada labaran Saudiyya (SPA) ne ya cewa ofishin ne ya fada ranar Talata. 
Haka kuma bangaren sanya maganin kashe kwayoyin cuta da kula da shimfidar masallaci na ofishin na aiki tukuru wajen tsaftace babban masallacin a kowacce rana ta hanyar yin amfani da sinadarai ba masu cutarwa ba, don tabbatar da cewa harabar da kuma al’umma ba su cutu ba. 
Ana saftacewa da goge-gogen ne domin kare masallata da masu ziyara zuwa Masallacin Haramin ta hanyar kashe dukkan kwayoyin cuta da suka makale a ciki da wajen masallacin. 
Wannan wani bangare ne na matakan kariya da a ke aiwatarwa don kariya daga kamuwa da cutar coronavirus (COVID-19) a babban masallacin da gine-ginen sa da kuma kewayen sa. 
Dadin dadawa, an raba tawogar ma’aikatan tsaftar, wadan da a ka yi musu horo na musamman domin wannan aikain, zuwa kashi uku kuma zasu rika yin aikin karba-karba a tsawon awanni ashirin da hudu (24). 
Babban ofishin ya kara da cewa ta yi gwaji na hakika a kan irin sinadarai da ruwan kumfar da za a yi amfani da su kafin a fara aikin goge-gogen da feshin maganin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here