An nuna gamsuwa da shirye-shiryen Hajjin 2020 a Kano

0
252


Daga Jabiru A. Hassan, Kano
Jami’an kula da Aikin Hajji na yankunan kananan hukumomin jihar Kano 44 sun bayyana gamsuwar su bisa yadda hukumar jin dadin alhazai ta jihar ta ke aiwatar da shirye-shiryen aikin Hajjin 2020, tare da sanar da cewa hakan zai sanya a samu nasarar gudanar da Hajjin bana cikin nasara.
Wannan bayani ya fito ne daga jami’in alhazai na karamar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Shehu Datti a zantawar su da Hajjreporters Hausa ranar Juma’a
Datti ya jaddada cewa “daga yadda aka fara shirye-shiryen Hajjin bana a Kano, da yardar Ubangiji za’a yi aiki mai tsafta kuma cikin nasara duba da yadda su kansu maniyyatan suke fahimtar tsare-tsaren aikin Hajji.”
Datti ya kara da cewa maniyyata da ke yankunan kananan hukumomi 44 na jihar Kano suna samun horo da ilimantarwa kan aikin Hajji, musamman yadda ake basu bitoci da wayar da kai kan ka’idojin aikin da dokokin kasar da za su da kuma makamar ita kan ta tafiyar wanda hakan abin jin dadi ne.
Dangane da maganar biyan kudaden ajjiya kuwa, Alhaji Datti ya ce maniyyata su na kokari sosai wajen kai kudaden su,  inda ya bada misali da cewa a karamar hukumar sa ta Dawakin Tofa akwai maniyyata fiye da 35 da suka bada nasu kudin ajjiyar, sannan kuma su na cika dukkanin sharuddan da aka sanya musu cikin biyayya da sanin ya kamata.
Jami’in alhazan ya godewa hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano bisa jagorancin Alhaji Mohammed Abba Dambatta, duba da yadda hukumar ta ke kara damarar gudanar da Hajjin bana cikin nasara.
Ya kuma yabawa jami’ar hulda da jama’a ta hukumar, Hajiya Hadiza Abbas Sanusi saboda aikin wayar da kai da ofishin ta ke yi kan aikin Hajjin bana da dokokin sa.
A karshe Alhaji Shehu Datti ya nuna farin cikin sa dangane da kirkiro kafar yada labaran aikin Hajji da Umara a harshen Hausa watau Hajjreporters Hausa, wanda hakan zai kara taimakawa wajen isar da sakonnin da su ka shafi aikin Hajji da Umara ga maniyyata, tareda yin kira ga maniyyata da su kara kasancewa masu bin dokoki kamar yadda su ka saba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here