Masari ya yabawa Ayade kan baiwa dan Jihar Katsina shugabancin Hukumar Kula da Alhazai ta C’River

0
201

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya yabawa Ben Ayade a kan nada dan asalin Jihar sa, Alhaji Rabilu Maimaje Abdullahi a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Alhazai ta Jihar Cross River. 
A kwanan nan ne dai Gwamna Ayade ya nada Alhaji Abdullahi a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Alhazai din ta Jihar Cross River 
Sabo da haka, yabawar ta zo ne a wata takardar taya murna zuwa ga Alhaji Abdullahi, mai dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Mustapha Muhammad Inuwa. 
A wasikar, Inuwa ya ja hankalin Abdullahi da ya ba mara da kunya wajen tafiyar da aikin sa cikin gaskiya da rikon amana. 
“Bayan godiya da jinjina ga Mai Girma Gwamna, farfesa Ayade, mu daga nan Katsina mun yi farinciki da gagarumar nasarar da ka samu kuma muna maka addu’a da Allah Ya sa ka yi aiki tukuru cikin gaskiya da rikon amana kamar yadda Mai Girma Gwamnan ya yi maka kyakkyawan zato da ma daukacin al’ummar musulmi da ma kafatanin mutanen Cross River,” SSG din ya ce. 
Inuwa ya kuma bayyana jin farincikin da Masari ya yi kan nadin Abdullahi, in da ya suffanta shi da cewa wakili ne nagartacce. 
“A madadin daukacin al’ummar Jihar Katsina, Mai Girma Gwamna Aminu Bello Masari, CFR, mu na taya ka murnar nadin da Farfesa Benedict Bengioushuye Ayade ya yi maka a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Alhazai ta Jihar Cross River. 
Wannan mukamin ya dace da kai ya kuma nuna cewa kai wakili ne na gari wanda nagartar sa ta sanya ya samu karbuwa a cikin al’ummar da ya ke zaune

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here