Sana’o’i, matafiya za su tafka asara idan COVID-19 ta hana aikin Hajji

0
228

Muhammad Siddique ya shafe shekaru biyar ya na tara kudin zuwa aikin Hajji a Makka, amma yanzu cutar nan ta COVID-19 ta sanya shirin nasa ya zama tana kasa tana dabo. 
Aikin Hajji na daya daga cikin musulunci da a ke son ko wanne musulmi ya cika. A na tsammanin ko wanne musulmi da ya ke da kudi da lafiya da ya yi wannan bulaguron zuwa Makka a kalla sau daya a rayuwa a tsawon watanni 12 na shekara, in da a bana ibadar za ta zo ne a watannnin Yuli da Agusta. 
Amma bayan Saudi Arebiya ta rufe hanyoyin sufuri zuwa kasa mai tsarki ga maniyyata Umara a watan jiya, yawancin maniyyatan na fargabar ko matakin zai shafi aikin Hajji. Ko a shekarar 1918 da a ka samu annobar cutar mura wacce ta kashe miliyoyin al’umma a fadin duniya, ba a dauki matakin fasa yin aikin Hajji ba kuma ba a taba fasawa ba a tarihi. 
“Idan tana ci gaba da yaduwa, to gara na yi asarar kudi da a ce ba zan je aikin Hajjin bana ba,” in ji Siddique, wanda ya biya dalar amurka dubu shida ($6,000) kudin ajiya da ba za a dawo da su ba,  ya biyawa kan sa da kuma mutum biyu a dangin sa. 
“Dole mu dauki matakan kariya”, in ji shi, ya kuma kara da cewa zai fasa tafiyar idan har cutar COVID-19 ta fara kama mutane da yawa a Saudi Arebiya. 
Tuni Gwamnatin Saudiyya ta takaita tafiye-tafiye zuwa cikin kasar bayan da cutar coronavirus din ta fara yaduwa a kasashen Gabas ta Tsakiya. Ranar Lahadi kasar ta sanar da rufe masallatai da kuma yiwuwar kin yin sallar Juma’a. 
Su ma matafiya daga kasar Canada na cikin damuwa: Gwamnatin kasar ce ta gargadi ya’n kasar da su tsai da duk wasu tafiye-tafiye da ba na dole ba a karshen makon da ya gabata, ta kuma kira ya’n kasar mazauna kasashen waje da su hanzarta su dawo gida tun kafin ta rufe iyakokin ta. 
Kuma Haji ba ibada ba ce mai arha. Farashin da a ka zayyana a yanar gizo-gizo na ibadar da ake kwashin makinni ana yi ya fara ne daga dala dubu goma ($10, 000) zuwa dala dubu goma sha biyar ($15,000), da kuma wasu tsare-tsare na masu hannu da shuni. Mutane da dama ne su ke tarin kudade domin tafiyar. 
Abdalla Ali, Babban Mashawarcin Al’umma na Kungiyar Musulmai ta Arewacin Amurka, ya ce kokarin da a ke na fasa yin aikin Hanjin bana wani abu ne da ba a taba yi ba a tarihi. Amma ya yarda cewa hakan ka iya faruwa a wani mataki na kariya da Gwamnatin ta rigaya ta dauka. 
“Wannan bai taba faruwa ba, amma da alama zai iya faruwa a bana sabo da har sun rurrufe jami’o’i da makarantu da sauran manyan wurare,” in ji Ali. 
Ya kara da cewa bayan da matafiya ka iya tafka asara a kan kudaden da su ka riga su ka biya, Ma su Harkokin Sufurin Jiragen Sama da ke kasar Canada ka iya fuskantar asara ta kudade suma idan har Gwamnati ta soke aikin Hajjin bana. 
 “Za su yi asarori da yawa,” in ji Ali, inda ya gano cewa kamfanunuwa da dama za su tafka asara a kasar idan farashin dalar Canada da riyal din Saudiyya su ka yi tashin gwauron zabi,”
“Ina ji a jiki na ma wasu daga cikin su za su tsiya ce,” in ji shi. 
Kamfanunuwan Sufuri da su ke harkar zuwa aikin Hajji na kasar Canada sun ce suna ta karbar kostomomi da su ke fasa tafiyar aikin Umara da Hajji.
 Mahad Warsame, Babban Jami’i a Sahal Umara da Hajji, ya kiyasta cewa a kalla mutane dari da hamsin ne su ka soke zuwa aikin Hajji tun  bayan Bullard coronavirus. 
“Wannan wani ibtila’i ne. Wani mawuyacin hali ne mu ke ciki har ta kai ga an fara kwantar da mutane,” in ji Warsame. 
“Mu na cikin wani hali na tsoro, kuma ba wai maganar harkar kudade bane, magana ce a ke ta cewa rayukan mutane na tafiya,”
Amma Warsame din ya ce ya na da yakinin cewa ba za a soke aikin Hajjin na bana ba. 
“Wannan cutar na da kamanceceniya da SARS, kuma Gwamnatin Saudiyya ta tare ta da gaggawa kuma da kuma kwazo wajen kare al’umma,” in ji shi, ya kuma kara da cewa an taba yin aikin Hajji ana tsaka da wata annoba a shekarar dubu biyu (2000). 
Yayin da akwai sauran watanni kafin zuwan aikin Hajjin, Ali ya ce akwai wajen mutane dari biyar (500) a masallacin yankin su da su ke fatan komai zai daidadita nan da ya’n makonni ma su zuwa. 
“Ni a kan kaina ina ganin Saudi Arebiya za ta yi iya bakin kokarin ta don ganin cewa ba a soke aikin Hajjin na bana  ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here