Hajjin 2020: India za ta fara jigilar alhazai ranar 9 ga Yuli

0
5

Kwamitin aikin Hajji na kasar India ya fitar da jadawalin jigilar alhazai na aikin Hajjin 2020.
Kamar yadda jadawalin ya nuna, alhazan za su fara tashi ne ranar 9 ga watan Yuli sannan su fara dawowa gida ranar 13 ga Agusta. 
Shugaban kwamitin aikin Hajji na Telangana ya bayyana cewa alhazan jihar za su fara dawowa gida daga kasa mai tsarki ranar 13 ga Agusta zuwa 3 ga Satumba. 
A kan cutar coronavirus kuma, an daga horas da alhazai a sansanonin su. 
Amma kuma za a bude sansanonin horaswar a watan Afrilu idan komai ya yi daidai. 
Ya kuma ce mamiyyatan Jihar za su iya cike ragowar kudin aikin Hajjin su da su ka fara biya kafin 31 ga watan Maris. Za su bayar da Rs1 lac, 20,000 na kudin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here