COVID-19: A sa da mu a tallafin biliyan 50 da a ka bayar- Masu harkar Hajji da Umara

0
216


Daga Mustapha Adamu
Kungiyar Masu Harkar Hajji da Umara ta Kasa ta roki Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari da ya sa Babban Bankin Kasa (CBN) ya hada da ya’n kungiyar a tallafin naira biliyan 50 da a ka bawa masu harkar otel da tafiye-tafiyen jirgin sama, da sauran harkoki, sakamakon bullar cutar coronavirus. 
Da ya ke wannan kira gaske Shugaban Kasa lokacin da Kungiyar Wakilan Kafafen yada Labarai ta Kano ta kai masa ziyara ta musamman a ofishin sa ranar Talata, Shugaban kungiyar, Alhaji Abdulaziz Halliru Kafinsoli ya yi korafin cewa bullar cutar COVID-19 ya haifar musu da asarar biliyoyin nairori. 
Shugaban ya kuma alakanta dakatar da Aikin Umara da Gwamnatin Saudiyya ta yi da cewa ya janyo musu asrar miliyoyin dalar Amurka, in da ya nuna cewa su ma sun cancanci Babban Bankin Kasa ya basu tallafin na rage radadi duba da cewa su na samarwa gwamnati haraji mai yawa. 
Kafinsoli ya ce”mun yi nazari a kan wannan tallafi da Babban Bankin Kasa zai bayar, amma ba mu da yakinin cewa za mu amfana daga tallafin sabo da har yanzu ba a tuntube mu ba.
“Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta duba ya’n kungiyar mu domin mun fi kowa yin asara daga bullar cutar COVID-19. Ya kamata a rika hadawa da mu a irin wadan nan tsarikan na gwamnati duba da irin dumbin harajin da mu ke kawowa gwamnati ta hanyar harkokin mu,

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here