COVID-19: Dakatar da Umara abin tashin hankali ne-Sheikh Hafiz

0
6


Daga Jabiru A. Hassan, Kano
Wani malamin addinin musulunci a Jihar Kano, Sheikh Hafiz Ibrahim Inyass Dawanau ya ce akwai tashin hankali da a ka dakatar da aikin Umara sakamakon bullar cutar coronavirus. 
Gwamnatin Saudiyya ce ta dakatar da aikin Umara da kuma shige da ficen jirage har zuwa lokacin da ta shawo kan yaduwar cutar a fadin kasar. 
Sabo da haka Sheikh Hafiz ya bayyana cewa “akwai tashin hankali ne ace zuwa aikin Umara ya sami tangarda saboda wannan cuta wanda hakan ya tauye wasu ginshikan aiyukan ibada ga al’umar musulmin duniya dake da ikon zuwa wannan ziyara mai albarka.”
Ya kuma yi kira ga musulmin duniya da su kara himma wajen yin addu’oi na neman tsari daga cutar nan mai sarke numfashi ta coronavirus wadda take neman kassara komai ciki har da sha’anin ibada da tafiye-tafiye.
Sheikh Hafiz ya kuma nunar da cewa  “babu abin da ya kamata  sai mu kara ci gaba da addu’oi domin rokon ubangiji madaukakin sarki ya kawar da ita daga doron kasa, sannan yana dakyau mu kara zage damtse wajen bautawa Allah da kaucewa dukkanin wasu laifuka da ke jawo manager annoba a duniya baki daya”. Inji shi.
Daga karshe, Sheikh Hafiz Ibrahim Inyass Dawanau ya yi fatan cewa  wannan annoba za ta zamo tarihi cikin kankanen lokaci ta yadda za’a samu sukunin ci gaba da gudanar da shirye-shiryen aikin Hajjin bana cikin kwanciyar hankali da nasara

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here