…Ta ce yada jita-jita ya fi coronavirus illa
Daga Mustapha Adamu
Ma’aikatar Lafiya ta Kasar Saudi Arebiya ta yi gargadin yada jita-jita, in da ta ce jita-jita ya fi cutar coronavirus illa sabo da yana haifar da tsoro na ba gaira ba dalili.
Yayin da yake ganawa da manema labarai a Riyadh ranar Talata, Dr. Mohamed Abdel Ali, kakakin ma’aikatar ya roki al’umma da su dena yada jita-jita, in da ya yi kira da a rika zuwa ma’aikatar a kan duk wasu bayanai kan cutar.
“Duk wasu fefayen rediyo da na bideyo da a ke yadawa a kan coronavirus a kasar nan da ba ma’aikatar mu ce ta sanar ba to ba gaskiya ba ne,” in ji shi, sai kuma ya gargadi masu ta’dar yada jita-jita da su dena ko su fuskanci fushin hukuma.
Kakakin ma’aikatar ya kuma ja hankalin al’umma da su guji wuraren taro sabo da an fi kamuwa da cutar ta wajen taron jama’a.
Abdel-Ali ya ce mutum 106 da a ka tabbatar cutar ta kama na da alaka ne da tafiya kasashen waje da su ka kai wajen kasashe ashirin.
“A cikin mutune 133 da da su ka kamu duk suna samun sauki sai mutum daya kawai,” in ji shi.
Abdel-Ali ya kuma gano cewa ba a samu bullar cutar a makarantun kasar ba. “Sama da mutum dubu dari bakwai (700, 000) ne a ka yi wa gwaji a hanyoyin shigowa kasar daban-daban. A na kuma daukar kwararan matakai na dakile yaduwar cutar