COVID-19: Saudiyya ta dakatar da yin salla a harabar Haramin Maka da Madina

0
212Gwamnatin Saudi Arebiya ta dakatar da shiga da kuma yin salla a wajen harabobin Masallacin Harambe Maka da na Madina, musamman ranar Juma’a, a wani bangare na matakan da kasar ke dauka wajen dakile yaduwar cutar koronabairos, in ji kakakin Ma’aikatar kula da Babban Masallacin Annabi ranar Juma’a. 
“Hukumomi, jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya ne su ka yanke shawarar dakatar da shiga da kuma yin salla a harabobin Masallacin Harami na Maka da na Annabi a Madina tun daga ranar Juma’a, 20 ga watan Maris. 
“Wannan wani mataki ne na dakile yaduwar cutar Koronabairos,” in ji kakakin a wata sanarwa ta kafar sadarwa ta twitter. 
Amma kuma, IHRHausa ta jiyo daga bakin wani dan Jihar Kano da ke zaune a Maka cewa jami’an tsaro duk sun tare hanyoyin zuwa Harami na Maka, inda ya ce kuma su na ta koro mutanen da su ke kokarin zuwa Masallacin domin yin sallar Juma’a. 
Ya ce yanayin abin tashin hankali ne sabo da ko a masallatan unguwanni ma an hana yin sallar jam’i, in da ya kara da cewa sai dai kawai a yi kiran salla a masallatan amma ba za a yi sallar a jam’i ba. 
“Abin sai dai innalillahi wa inna ilaihi raaji’un. Duk wadan da su ke zuwa Harami an koro su. Jami’an tsaro ne su ke koro mutane kuma duk sun rurrufe hanyoyi. 
” Ko a masallatan unguwa ma sai dai a yi kiran sallah amma ba za a yi sallar ba. Wannan abin yana tayar mana da hankali yanzu a ce an wayi gari ba za ai sallar Juma’a ko jam’i a Maka?,”
Sai dai kuma IHRHausa ta rawaito cewa an yi sallar Juma’a din a Haramin Maka, amma ba ta da masaniyar ko an bar jama’a sun shiga ko ba su shiga ba cikin harabar ba, duba da dakatarwar da a ka yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here