Hajjin 2020: Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Abuja ta dakatar da bita

0
237

Hukumar Jin dDadin Alhazai ta Abuja ta sanar da dage bitar aikin Hajjin bana wanda da ta shirya za a gabatar a gobe Asabar da kuma Lahadi.
Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a yace dakatar da bitar ya zama wajibi saboda umarnin da Gwamnatin Abuja ta bayar na hana gabatar da duk wani taro da zai tara jama’a da yawa a waje daya don kauce wa yaduwar annobar coronavirus.
Jami’in ya rarrashi maniyyatan bisa ga rashin jin dadin da dakatarwar za ta haifar musu. 
Yace za a sanar wa alhazan sabuwar ranar da za a yi bitar da zarar al’amura sun daidaitu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here