Daga Mustapha Adamu
Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), Alhaji Zikrullah Olakunle Hassan ya ce hukumar na da yakinin cewa za a yi Aikin Hajjin bana.
Alhaji Hassan ya bayyana hakan ne jiya a fadar Shugaban Kasa a Abuja lokacin da ya ja ragamar ma’aikatan domin yi wa Shugaba Muhammadu Buhari godiya a kan nadin da ya yi musu, da kuma yi masa bayani a kan shirye-shiryen da hukumar ke yi na Aikin Hajjin bana.
Ya kuma kara da cewa hukumar ba za ta yi sako-sako ba wajen shirin sabo da cutar kare dangin nan wato COVID-19, wacce a ka fi sani da coronavirus.
Da a ka tambaye shi a kan shirin da ya ke yi domin dakile kamuwa da cutar coronavirus idan ba ta yi sauki ba har zuwa lokacin Aikin Hajjin, sa ya ce” Game da cutar COVID-19, a matsayin mu na ma su imani muna da yikini a zuyiyoyin mu a ko da yaushe, amma duk da haka ba za mu yi sakaci ba.
“Ina mai tabbatar muku da cewa mu na aki kafada da kafada da Ma’aikatar Lafiya ta Kasa domin tabbatar da burin gwamnati a kan cutar,”
“A cikin mu a kwai wanda ya ke tare da Ma’aikatar Lafiya. A ko wacce rana muna tattaunawa a kan sanin takamemen abubuwan da su ke faruwa. Ina mai tabbatar muku da cewa ba za mu saba duk wasu sharudda da da gwamnati ta gindaya domin tabbatar da cewa ya’n kasa a ciki da wajen kasar sun samu cikakkiyar lafiya da kuma kariya.
” In Allah Ya yarda sai an yi Aikin Hajjin bana,” in ji Alhaji Hassan.