Yanzu-yanzu: Mutane 8 sun kara warkewa daga coronavirus a Saudiyya

0
225


Karin mutane takwas (8) sun warke daga cutar coronavirus. Ya zama kenan mutane goma sha shida (16) ne suka warke daga cutar a kasar. 
Wannan labarin zai karawa musulman duniya kwarin gwiwar cewa za a yi Aikin Hajjin bana. 
Shi ma Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa, Alhaji Zikrullah Olakunle Hassan ya bayyana yakinin sa na cewa cutar coronavirus ba za ta hana Aikin Hajjin na bana ba. 
Ya kuma kara da cewa hukumar na iya kokarin ta na tabbatar da kariya ga mahajjatan ta a kasa mai tsarki, daidai da sharuddan da Ma’aikatar Lafiya ta kasa ta gindaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here