Hajiin 2020: An bude shafin yin rijista da tawogar ma’aikatan lafiya ta NAHCON ga masu sha’awa

0
7

Daga Mustapha Adamu
Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta bude shafin yanar gizo na Tawogar Ma’aikatan Lafiya domin yin rijista ga wadan da su ke da sha’awar yin aiki a cikin tawogar a yayin Aikin Hajjin 2020. 
Ga sharudda nan a kasa da za ku bi don samun shafin yin rijista din ta yanar gizo: 
Ka karanta sharuddan: 
1- Idan za ka fara rijista din sai ka fara kirkiro da manhaja taka ta kan ka. 
2- Yayin kirkiro da manhajar, ka tabbata ka yi amfani da sahihin adreshin ka na aika sakon yanar gizo. 
3- Yi amfani da adreshin aika sakon da kuma lambar sirrin ka a matsayin bayanan bude manhajar. 
4- Ka tabbata ka bayar da sahihan bayanai yayin yin rijistar. 
5- Ka tabbata ka yi bitar bayanan ka kafin ka aika. 
6- Ka tabbata ka aika bayanan sau daya tak domin aikawa sama da daya zai sanya a cire ka daga tsarin. 
Domin tambayoyi, ka aika sako ta kafar aika sako ta yanar gizo zuwa: 
Idan za ka aika ka yi amfani da wannan adreshin da ke kasa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here