Daga Jabiru A. Hassan, Kano
Kwararru kan aikin kula da lafiyar al’umma da kuma malamai masu gudanar da fadakarwa kan al’amuran yau da kullum sun bayyana cewa da yardar Ubangiji an kusa dakile annobar cutar coronavirus a fadin duniya, musamman ganin yadda gwamnatoci da shugabannin kasashen duniya suka mayar da hankali kan kawar da cutar.
HajjreportersHausa ta gudanar da wata ganawa da wasu kwararrun likitoci da kuma malaman addinin musulunci kan halin da duniya ta shiga musamman yadda al’amura suke kawo tsaiko wajen shirye-shiryen zuwa umara da kuma aikin Hajjin 2020.
Dokta Nafiu Yakubu Mohammed Tofa, wani kwararren likita a Kano ya ce ” duba da yadda ake daukar matakai na dakile wannan annoba ta cutar Coronavirus, ina kyautata zaton cewa an kusa kawo karshen ta a fadin duniya baki daya. Sannan akwai alamun cewa musulmin duniya zasu sami damar gudanar da aikin Hajjin bana cikin nasara,” inji shi.
Shima a nasa tsokacin, wani masani kan aikin bincike da hada magunguna, Dokta Umar Likita ya ce yanzu duniya ta tashi tsaye wajen nemo bakin zaren kawar da wannan cuta, don haka yana da kyau gwamnatocin kasashen duniya su kara baiwa masanan su cikakkiyar damar gudanar da bincike da samar da ingantattun magungunan wannan cuta baki dayan ta.
A nasa tsokacin, wani malami mai fadakarwa, Sheikh Usman Abdullahi Santa yace manyan malamai da masu bincike na musulunci sun tabbatar da cewa annoba tana iya faruwa a duk lokacin da Ubangiji ya nufa, don haka Coronavirus ta kasance daya daga cikin abubuwa masu kama da annoba kuma da ikon Allah za ta zama tarihi.
Dukkanin wadanda HajjreportersHausa ta zanta da su sun bukaci al’umar musulmi, da ma wadanda ba musulmi ba da a kara addu’o’i domin neman tsari daga cutar, tare da yabawa Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da dukkanin hukumomin kula da jin dadin alhazai na jihohi bisa kokarin da suke yi wajen gudanar da aiyukansu duk da cewa ana cikin kalubale na harkar lafiya a duniya baki daya