Daga Mustapha Adamu
Gwamnatin Saudi Arebiya ta ce ba ta yanke hukunci a kan ko za a yi Aikin Hajjin 2020 ko ba za a yi ba.
Wannan batu ya fito ne daga bakin Abdullah Ahmad Al Abdan, wakilin Saudiyya a Senegal, a yayin taron manema labarai.
Akwai damuwa cewa cigaba da yaduwar cutar coronavirus ka iya sanya kasar ta dakatar da Aikin Hajjin bana zuwa wata shekarar, kuma wannan mataki ne da ba a taba ganin sa ba a tarihi.
A makon karshe na watan yuli ne dai za a fara ibadar Hajjin na bana.
Sabo da haka Al Abdan ya shawarci kamfanunuwan da suke shirya Aikin Hajji da su dakata kulla yarjejeniya da masu otal da kamfanunuwan jigilar jiragen sama har sai an bada sanarwa daga mahukunta.
Tun da farko ne dai kasar ta dakatar da bada bizar Umara domin dakile yaduwar cutar.
Ta kuma dakatar da sallolin jam’i Masallacin Harami da Masallacin Annabi, masallatai mafi tsarki da ke a Maka da Madina.
“Kawo yanzu, Saudi Arebiya ba ta yanke hukunci kan dakatar da Hajjin bana ba, amma kowa ya shirya bin duk wani hukunci da kasar za ta yanke.
” Wannan shine magana, sabo da kada mutane su shiga wani yanayi da ba za su iya jurewa matsakar da hakan ka iya haifarwa ba,” in ji Al Abdan.