Daga Mustapha Adamu
Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta umarci Hukumomin kula da Jin Dadin Alhazai na Jihohi da su dakatar da yin bita ga maniyyata sakamakon ci gaba da yaduwar cutar COVID-19, wacce a ka fi sani da coronavirus.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shugabar Fannin Hulda da Jama’a na hukumar, Fatima Sanda Usara ta ce “NAHCON din ta fitar sanarwa mai lambar NAHCON/SB/33/VOL.XVIII/260 ga daukacin Hukumomin Kula da Jin Dadin Alhazai, da ma’aikatun kula da Aikin Hajji da su dakatar da bita har sai abin da hali ya yi.”
Umarnin ta zama dole duba da irin barazanar da cutar COVID-19 ke haifarwa wajen yiwuwar yaduwa cikin sauri a cinkoson jama’a. Ita kuwa NAHCON ta damu da kare lafiyar mahajjata da maniyyata a ciki da wajen kasar nan.
Bugu da kari kuma Gwamnatin Tarayya, ta hannun Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Kasa ta hana duk wani taro na jama’a har da ma na addinai. Gwamnatin ta yi haka ne domin karfafa umarnin warewa tsakanin jama’a a wani mataki na dakile yaduwar cutar COVID-19. NAHCON kuma ta yi riko da wannan matakin.
Sanarwar, wacce kwamishinan tsare-tsare, bincike, kididdiga, bayanai da ajiye bayanai na NAHCON, Sheikh Suleman Momoh ya sa hannu, ta jinjinawa Hukumomin Kula da Jin Dadin Alhazai na Jihohi kan kokarin da su ke yi na wayarwa da maniyyata kai. Bitar na da muhimmamci gurin horas da ma alhazan Nigeria su zama wakilai na gari a Saudi Arebiyya.
Amma kuma sanarwar ta bada shawarar a ci gaba da gudanar da duk wasu shirye-shirye na Aikin Hajjin bana.