Daga Jabiru A. Hassan, Kano
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano zata ci gaba da yiwa maniyyatan jihar bitoci ta kafafen yada labarai domin ci gaba da bada horo kan yadda Aikin Hajji yake da ka’idojin sa.
Wannan matakin ya zo ne sakamakon yadda annobar cutar Coronavirus ta ke daukar sabon salo, wanda dole sai an kauracewa cunkoson al’uma baki daya.
Jami’ar Hulda da jama’a ta hukumar, Hajiya Hadiza Abbas Sanusi ita ce ta shaidawa wakilin mu hakan da yammacin ranar Juma’a.
Jami’ar ta sanar da cewa ” bisa umarnin da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa, NAHCON, ta bayar na dakatar da dukkanin wasu tarurruka na bitoci ga maniyyata. Muma a matakin jihar Kano kuma bisa umarnin maigirma babban sakatare na hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Kano mun dakatar da dukkanin bitoci har sai al’ amura sun inganta, ” Inji ta.
Hajiya Hadiza ta kuma shaidawa Hajjreporters Hausa cewa akwai cibiyoyin bita 16 a fadin jihar ta Kano, sannan dakatarwar da a ka yi ta sanya za’a ci gaba da wannan bitoci ta kafafen yadda labarai ta yadda maniyyatan za su kara samun kwarewa kafin babban taron bita kamar yadda a ka saba duk shekara, tare da yin kira ga maniyyatan da su ci gaba da yin addu’oi na neman karshen wannan annoba ta Covid-19.
A wani cigaban kuma, wakilin mu ya rawaito cewa an gudanar da sallar juma’a a a masallatan dake fadin jihar Kano, inda kuma aka yi addu’oi na musamman domin neman tsari daga dukkanin wata annoba dake girgiza duniya,tareda yin addu’ar samun damar gudanar da Hajjin bana cikin kwanciyar hankali da lafiya.