Gwamnatin Saudi Arebiya ta sanar da cewa mutune sittin da shida (66) ne su ka warke daga cutar coronavirus a kasar.
An wallafa sanarwar ne a shafin kafar sadarwa ta twitter na jaridar Saudi Gazette, babbar jaridar ingilishi a Saudi Arebiya.
An kuma rawaito cewa an kuma samun sababbin mutane 96 da su ka kamu da cutar, in da adadin wadanda su ka rasu ya kai mutan takwas (8)