Bayan kwanaki 11, an sake bude Ka’aba domin dawafi

0
277


Daga Mustapha Adamu
An sake bude Ka’aba domin yin dawafi, bayan kwanaki goma sha daya (11) da rufewa, amma mutane kadan a ke bari su shiga su yi ibada. 
A tuna cewa, ranar ashirin ga watan Maris, Masarautar Saudi Arebiya ta fitar da dokar hana yin dawafi a kewayen Ka’aba sakamakon bullar cutar nan da ta game duniya, wato coronavirus. 
Shafin kafar sadarwa na Haramain ne ya wallafa cewa an dawo da yin dawafi, amma rukunin mutane kadan za a rika bari suna yin ibada a wajen mai tsarki. 
A wani bangaren kuma, Ministan Kula da Aikin Hajji na kasar ya ce sun kammala duba ingancin otal-otal da su ke birnin Makka. 
“Dukkanin alhazan da ba za su iya komawa kasashen su ba sabo da rufewa da a ka yi to za a basu otal-otal ma su darajar tauraro 5, gami da kula da lafiyar su,  inshorar rayuwar su, shawarwari da sauran su. Za a ci gaba da kula da su a tsawon lokacin da ya kamata,”
Ga rage yawanmutanen da su ke dawafi kuma, Ministan ya ce wani mataki ne na kariya sabo da ba a so yanayin ya kazance sama da a yadda ya ke a halin yanzu. 
Ya kuma bayyana cewa duk wadan da su ka biya kudin Umara an dawo musu da kudaden su. 
Ministan Hajjin ya kuma yi kira ga duk kasashe da su dakata a kan dukkan wasu shirye-shirye a kan aikin hajji har sai komai ya daidaita. 
“Ya yi wuri a ce an cimma matsaya. Sabo da haka za a bayyana matakin da a ka dauka idan lokacin hajjin ya karato

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here