Daga Jabiru A. Hassan, Kano
Kungiyar Ma su Bada Rahoton Aikin Hajji Da Umara (Independent Hajj Reporters) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sanya kamfanoni ma su harkar Hajji da Umara cikin jadawalin fannonin da za ta baiwa tallafi sakamakon hasarar da annobar cutar COVID-19 ta haifar.
A cikin wata sanarwa da kodinetan kungiyar na kasa, Malam Ibrahim Mohammed ya sanya wa hannu kuma a ka rabawa manema labarai, kungiyar ta yi bayanin cewa kamfanonin dake shirya tafiye-tafiye na aikin Hajji da Umara suma sun kasance suna da bukatar tallafi.
Kamafanonin, in ji cikin kungiyar, ya kamata a ce su na jerin wadanda su ke da bukatar tallafi da gwamnatin tarayya ta ware domin farfadowa tareda samun damar ci gaba da gudanar da harkokin su kamar yadda aka saba sabo da su ma annobar ta yi musu ta’adi sosai.
Sanarwar ta ce” ko shakka babu, dakatar da zuwa Umara da hukumomin kasar Saudiyya su ka yi ya kawo durkushewar tattalin arzikin kamfanonin shirya tafiye-tafiye na wannan kasa, Wanda hakan ya sanya muke fatan cewa gwamnatin tarayya za ta taimaka ta sanya su cikin jerin kamfanonin da za su amfana da wannan kudade da aka ware don tallafawa sakamakon bullar cutar Covid-19″. Inji Kungiyar.
Bugu da kari kungiyar ta Hajj reporters ta Sanar da cewa akwai kamfanonin shirya tafiye-tafiyen sama da 250 wadanda su ke cikin wannan sana’a, kana mutane fiye da dubu 20 ne ke cin abinci karkashin wadannan kàmfanoni.
Don haka, a cewar kungiyar, yana da kyau a dubi bukatun kamfanunuwan wajen shigar da su cikin wadanda za su amfana da wannan tallafi na naira biliyan 50 da a ka ware domin taimakawa fannonin da harkokin su su ka tsaya saboda annobar coronavirus