Daga Mustapha Adamu
Saudi Arebiya ta saka dokar hana fita kwata-kwata a biranen Makka da Madina, kuma tuni dokar ta fara aiki a ranar Alhamis, kamar yadda sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta kasar ta bayyana.
Ba wanda a ka yarda ya fita a birane biyun sai dai idan da wani kwakkwaran dalili da ya hada da siyan abinci ko zuwa asibiti, shi ma sai dai tsakanin karfe 6 na safe zuwa karfe 3 na rana. Kuma kowa a yankin unguwar sa a ka yarda ya fito.
An rufe duk wata hada-hadar kasuwanci a Makka da Madina tun daga yau (Alhamis). Shagunan sai da magani da kayan masarufi kadai a ka yarda su bude.
A makon jiya ne Sarki Salman bin Abdul’aziz ya amince da matakin a rufe biranen Riyadh, Makkah da Madina kuma har yanzu dokar tana aiki. Har yanzu an hana mutane shiga ko fita daga biranen.
Ma’aikatar ta kara jaddada cewa dokar hana fitar ba ta shafi wadan da su ke aiki a muhimman ma’aikatu na gwamnati da ma su zaman kan su da su ka hada da jami’an tsaro, sojoji da kafafen yada labarai. Haka kuma su ma ma’aikatan lafiya dokar ba ta shafe su ba.
Zuwa ranar Alhamis, adadin mutane 1,885 ne su ka kamu da cutar coronavirus a Saudi Arebiya, in da mutane 21 su ka rasa rayukan su, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta kasar ta bayyana.
Haka kuma a adadin mutanen da su ka kamu da cutar a kasar, mutane 328 sun warke.