Limaman Kano sun yi addu’ar kawo karshen COVID-19 da samun damar yin Aikin Hajji

0
7


Daga Jabiru A. Hassan, Kano
Limaman masallatan Juma’a a Jihar Kano sun gudanar da addu’oi na musamman domin  ganin annobar coronavirus ta zamo tarihi a fadin duniya baki daya, tare da fatan ganin an samu damar gudanar da Aikin Hajjin wannan shekara cikin kwanciyar hankali da koshin lafiya.
Wakilin Hajjreporters Hausa ya samu damar ziyartar wasu limamai jim kadan bayan kammala sallar Juma’a, inda su ka bayyana cewa wannan annoba ta Covid-19 tana bukatar addu’oi na musamman domin samun yardar Ubangiji wajen murkushe ta baki daya ta yadda duniya zata zauna lafiya kuma cikin kwanciyar hankali.
Sannan kusan dukkanin hudubobin da limaman su ka gabatar sun yi magana ne kan annobar da kuma bukatar da ake da ita na yin hakuri da jarrabawar da Ubangiji ya ke yiwa bayin sa tare da bin umarnin shugabanni da masana harkar kula da lafiya har sai an sami lafiya da kwanciyar hankali kamar yadda al’amura su ke tafiya a halin yanzu na  annobar coronavirus.
Malam Abubakar Ahmed, wanda ya gabatar da wata fadakarwa kan yadda limamai su ka himmatu wajen addu’oi, ya ce a jihar Kano ana yin addu’oi na musamman domin neman yardar Ubangiji wajen ganin an kawo karshen Covid-19 a fadin duniya, musamman ganin cewa wannan annoba ta shafi kowane addini da kuma jinsi.
Daga Karshe, limaman  masallatai da ke  Jihar Kano sun sanar da cewa za su ci gaba da gudanar da addu’oi domin ganin cewa  an gudanar da Aikin Hajjin bana cikin nasara bayan ganin wannan annoba ta Covid-19 ta zamo tarihi a fadin duniya.
Sun kuma gargadi al’umar musulmi da su kaucewa duk wani abu na sabawa Mahalicci wanda hakan yana daga cikin abubuwan da me sanyawa Ubangiji ke jarabtar bayin sa da annoba mai tada hankali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here