Ma’aikata 3,500, injina 89 ne ke feshin magani a Masallacin Harami a kullum

0
315

Daga Mustapha Adamu
Ma’aikata 3,500 ne da kuma injina 89 a ke amfani da su wajen yin feshin magani a Babban Masallacin Makka, wato Harami, kamar yadda Saudi Pres Agency (SPA) ta rawaito. 
Rahoton ya ce sama da lita 2,160 na sinadaran tsaftace muhalli ba masu cutarwa a ke amfani da su a lokuta shida da a ka ware domin goggoge ciki da ban Haramin. 
Bayan haka kuma, ana goggoge dukkanin shimfidun Masallacin sau daya a kwanaki biyar, SPA din ce ta ce Babban Jami’in kula da Masallatai Masu Alfarma guda biyu ne ya fada. 
A bangaren kula da zamzam kuma, wanda a kewa lakabi da Suqya, an saka ma’aikata 450 domin su rika tsaftace da tulunan ajiye zamzam, da famfuna da kuma rijiyar zamzam din ta amfani da sinadaran tsaftacewa. Akwai tulunan ajiye zamzam 27,000 a Masallacin Mai Alfarma. 
Bugu da kari, ofishin kula da ayyuka na Masallatai Masu Alfarma ya kuma feshe kujerun guragu masu amfani da wuta da marasa amfani da wuta da a ka ajiye su a dakin ajiye kaya. An kai safar hannu da sinadaran tsaftace muhalli a duk cibiyoyin aiki da ke ciki da wajen Masallacin.
Ofishin kula da Masallatai Masu Alfarman ya dauki wadan nan matakan ne domin kariya da kuma dakile yaduwar cutar kare dangin nan wato COVID-19 a ciki da wajen masallacin. Haka kuma ana daukar matakan ne domin kare masu ziyara da ibada a Babban Masallacin. 
An kasa masu aikin feshin gida uku kuma su na aikin karba-karba sau uku a cikin awanni 24 tsawon kwanaki 7 a cikin Haramin. Sai da a ka bawa wadan nan ma’aikatan horo na musamman da kuma wayar da kai a kan matakan kariya da kuma kare al’umma, kuma mafi muhimmancin feshin da a ke yi shine kare masu ziyara da masu ibada a Masallacin Mai Tsarki. 
Ana amfani da injina na musamman wajen gauraya sinadaran feshin da sabulai domin samun daidaito tsakanin sinadaran. An horas da ma’aikatan kan yadda za su gauraya sinadaran daidai wadaida. 
Dadindadawa, sai da a ka yi gwaji na musamman a kan sindaran kafin ma a fara wankewa da feshin da a ke yi a Haramin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here