Da dumi-dumi: Rigakafin coronavirus na daf da fitowa a Saudiya

0
6

Saudi Arebiya na kirkiro da wata allurar rigakafin cutar coronavirus, kuma ana daf da sanar da ita, in ji wani ma’aikacin lafiya. 
Dakta Hatem Makhdoom, mataimakin farfesa a cibiyar bincike da gano kwayoyin cututtuka kuma mataimakin shugaban fannin kimiyyar magunguna a Jami’ar Taibah ne ya bayyana cewa manuniyar ilimin kimiyyar yaduwa da dakile cututtuka ya nuna cewa Saudiya za ta samu daidaito da kuma tafiyar cutar coronavirus din zuwa karshen watan Afrilu. 
Ya yi wannan bayanin ne da a ke masa tambayoyi a wani shiri na kafar yada labarai ta Okaz-Podcast mai taken “Daga… Zuwa”.
Dakta Hatem ya ce ba a kamuwa da cutar coronavirus ta ya’n yatsu ko hannaye sai dai idan mutum ya taba wajen da cutar ta ke sannan kuma ya taba hancin sa, bakin sa ko idanun sa. 
Ya kuma bayyana cewa shirme ne a rika saka safar hannu lokacin zuwa kantunan saida kaya, in da ya ce “idan kuma shi mai shagon ya taba wayar hannun sa ki kuma wasu kayayyakin nasa bayan kuma ya taba wani guri mai dauke da kwayoyin cutar. 
” Menene amfanin safar hannu idan har mutum zai taba guri mai dauke da kwayoyin cutar sannan ya taba hanci, baki ko idanun sa, to kuwa dole ya kamu da kwayoyin cutar,”
Dakta Hatem ya yi bayanin cewa coronavirus na rayuwa ne a jikin jemagu kuma tana iya yaduwa zuwa wasu dabbobin ko jikin dan’adam. 
Akwai kwayoyin cututtuka hudu daga dangin korona da su ke haddasa mura da tari kuma mutane ba su maida hankali a kan su ba duk da cewa an gano hakan tun a shekarun alif dari da sittin. 
Ya kuma bayyana cewa Saudi Arebiya ta amfana sosai da irin fafautukar da ta yi wajen shawo kan annobar cutar  nan ta MERS ta wajen daukar matakan kariya gami da ilimin kimiyyar yaduwa da dakile cututtuka da kuma gwaje-gwaje da ta yi. 
“Duk da cewa ana samun karuwar masu kamuwa da cutar coronavirus, mun lura cewa yawan masu kamuwa da cutar a cikin ma’aikatan lafiya bai taka kara ya karya ba kuma a karshe dai an samu maganin hana kamuwa da cutar,” in ji shi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here