COVID-19: Ba za a yi sallar tarawi lokacin azumin Ramadan a Saudiyya ba

0
349

  

Hukumomin Saudiyya sun ce ba za a gudanar da jam’in Sallar Asham ko tarawi ba a Makkah da Madina idan har ba a kawo karshen annobar coronavirus ba.
Ministan ma’aikatar kula da harkokin lamurran addini a Saudiyya Dr. Abdul Latif Al Sheikh ne ya sanar da haka, a wata hira da kafar MBC da aka watsa a ranar Lahadi, kamar yadda jaridun kasar suka ruwaito.
Jaridar Saudi Gazette ta ambato ministan yana cewa: “dakatar da salloli biyar na farilla a masallaci ya fi dakatar da Sallar Taraweeh girma. Muna rokon Allah ya karbi ibadarmu ta Taraweeh a masallaci, ko a gida, wanda muke tunanin ya fi dacewa domin lafiyar al’umma.”
Ya kuma yi addu’a tare da fatan kawo karshen wannan annoba da wuri. Ya kuma roki Allah ya karbi ibadar musulmi ta Sallar Asham da za su gudanar a Masallaci ko gida.
Kazalika ya ce; “Sallar Jana’iza ma a makabarta za a dinga yin ta. Kuma kar mutane su taru sosai. Sauran mutane za su iya yi wa mamacin Sallar Jana’iza daga gidajensu”
Babu dai tabbas na gudanar da aikin hajji a bana, yayin da gwamnatin Saudiyya ta nemi kasashen duniya su dakatar da karbar kudaden jama’a domin zuwa aikin Hajji, a yayin da annobar coronavirus ke ci gaba da mamaye duniya.
Tuni hukumomin Saudiyya suka hana shiga Makkah da Madina, da ma Riyadh babban birnin kasar, a kokarin da hukumomin kasar ke yi na hana yaduwar Covid-19.
Hukumomin lafiya a Saudiyya sun ce zuwa yanzu mutum 4,462 suka kamu da cutar, yayin da ta kashe 59.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here