COVID-19: Da yiwuwar Saudiyya ta bar kashi 10 na alhazan ko wacce kasa su je Aikin Hajji

0
267

Ana tunanin Saudi Arebiya ta bar kashi goma na kowacce kasa daga cikin adadin alhazan da a ka yarje musu su je aikin Hajjin bana. 
Ministan Harkokin Addini da Wanzar da Zaman Lafiya tsakanin Mabiya Addinai na Pakistan,  Sahibzada Noor-ul-Haq Qadri, ranar Asabar ya baiyana cewa a tsakiyar watan Ramadan ne za a dau matakin yi ko barin aikin Hajjin bana, kuma daya daga cikin matakan sa za a iya dauka shine a bar kashi goma daga kowacce kasa su je aikin Hajjin 2020.
Wani rahoto daga wata jarida ta Pakistan din mai suna Associated Press of Pakistan ta fado abin da ministan ya ce a wata sanarwa cewa “ma’aikatar ta sa na tuntubar mahukuntan Saudiyya a kai-a kai  kuma suna ta shawarwarin matakin sa za su dauka da su ka hada da a bar alhazan Saudiyya din kawai su yi aikin Hajjin, ko su bar ya’n yankin kasashen larabawa kawai su je ko kuma kashi goma na kowacce kasa su je aikin Hajjin na bana. 
Sai dai kuma sai nan gaba za a dau matsaya guda daya bayan an tattauna da duk masu ruwa da tsaki, da kuma ganin an samu gagarumin sauki a kan coronavirus. 
Ya kara da cewa, Ministan Harkokin Aikin Hajji na Saudi Arebiya ya bawa Hukumar Kula Da Harkokin Addini da ta dakatar da shirye-shiryen Aikin Hajjin 2020 na wucin gadi sakamakon rashin tabbas din da annobar coronavirus ta haifar. 
Mahukuntan Saudiyya sun hana Pakistan din ta cimma yarjejeniya ta karshe da kamfanunuwan dafa abinci, masu gidaje, masu harkar sufuri da sauran su har sai sun kuma bada umarnin yin hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here