Abinda ya sa za a yi Aikin Hajjin bana-NAHCON

0
249

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ta bayyana dalilan da su ka sanya za a iya yin Aikin Hajjin 2020.
Shugaban hukumar, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da gidan Hukumar Rukunin Gidajen Rediyon Tarayya na Kasa a ofishin sa, a wata sanarwa da hukumar ta fitar. 
Alhaji Hassan ya bayyana kwarin gwiwa cewa bayanai da su ke fitowa daga Ma’aikatar Lafiya ta Saudi Arebiya na nuni da cewa kasar za ta fuskanci gagarumin raguwar cutar COVID-19 daga 21 ga watan Afrilu da kuma yiwuwar kore cutar kwata-kwata daga kasar a watan Mayu na 2020.
Ya ce, duba da wannan, hukumar sa na da kwarin gwiwar cewa za a yi Aikin Hajjin bana. 
“Hakan ne zai nuna maka dalilin da ya sanya NAHCON ba ta dakatar da shirye-shiryen Hajjin 2020 ba,” in ji shi. 
Ya kuma karfafawa maniyyata gwiwa da su ci gaba da biyan kudaden Aikin Hajji, in da ya fadakar da cewa za a iya samun karancin mahajjata a bana a wani yunkuri na dakile cutar ta coronavirus. 
“Idan haka ta faru, to za a bawa maniyyata kujerar Hajji ne ta amfani da wanda ya fara biyan kudi. 
Ya kuma karawa maniyyatan Hajjin bana karfin gwiwa da su kasance cikin shiri domin zuwa yin babbar ibadar. 
Shugaban ya kuma bayyana cewa duk da kwarin gwiwar da ta ke da shi, hukumar ta yi shirin ko ta kwana ne ko da Aikin Hajjin na bana ba zai yiwu ba. 
Haka zalika ya kara da cewa hukumar ta yi duk wata yarjejeniya da kamfanonin da ke gudanar da dawainiyar mahajjata a bisa doron doka, in da ya tabbatar da cewa hukumar ba za ta samu wata asara ta kudi ba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here