COVID-19: Kada ku bari annobar nan ta hana ku bautar Allah a Ramadan- Limamin Madina

0
246


Daga Mustapha Adamu
An yi kira ga musulmin duniya da kada su bari tsoron annobar COVID-19, wacce a ka fi sani da coronavirus ya hana su bautawa Allah Madaukakin Sarki a wata mai albarka na Ramadan. 
IHRHausa ta rawaito cewa musulmai ne a fadin duniya su ka fara ibadar azumi a watan Ramadan, sai dai kuma azumin na bana ya zo a yayin da yawancin kasashen duniya su ke fama da annobar coronavirus. 

A yayin da ya ke hudubar sallar Juma’a a Babban Masallaci Mai Tsarki na Madina, Limamin da ya ja sallar, Sheikh Ali Bin Abdur Rahman Al Huthaify ya ce da yardar Allah, komai daren dadewa cutar nan za ta tafi. 

A cewar sa, wannan tarin mutanen da su ke halartar kasa mai tsarki a duk shekara da ba su samu damar zuwa ba a bana sakamakon annobar coronavirus, za su dawo nan gaba da yardar Ubangiji. 
“Za mu tsallake wannan jarrabawar da yardar Allah. Kalli yadda masallacin nan ya ke ba kowa. To in Sha Allah nan gaba kadan dumbin jama’ar da ke zuwa ibada nan kasar za su dawo su ci gaba da zuwa,”
Limamin ya yi kira ga musulmai da su haskaka gidajen su ta hanyar yin sallolin tarawih tunda an hana fita zuwa masallatai, in da ya ce “kowa ya yi sallar a gida shi da iyalan sa. Hakan zai kara karfafa kaunar juna. Idan mutum bashi da iyali to ya yi shi kadai a gida”
“Kada mu bari wannan annobar ta hana mu yin ibada. Ku dai kawai ku bi ka’idoji da sharuddan kare lafiya da hukumomi su ka shimfida.
Ya kuma yi kira ga matasa da kada su bari wayoyin salula su dauke musu hankali wajen bautar Allah a wannan wata mai alfarma. 
“Ina kira da ku riki yin tsafta kamar yadda ma’iaki tsira da amincin Allah ya hore mu kuma shima yake aikatawa. 
” Ina rokon Allah da Ya yaye mana wannan annoba. Allah Ya bawa wadan da su ka kamu sauki. Mu kuma da bamu kamu ba Allah Ya kare mu. Allah Ya bamu ladan ibada,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here