Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na Jihar Kwara ya maida sansanin alhazai da ke Ilori, babban birnin jihar, zuwa cibiyar killace masu fama da cutar coronavirus a jihar.
A ranar Talata da daddare ne dai gwamnan ya wallafa a sahfin sa na kafar sadarwa ta twitter cewa cibiyar mai gadaje 600, za ta yi amfani ne wajen killace mutanen da su ka yi mu’amala da wadan da su ka kamu da cutar da a ke wa lakabi da COVID -19.
Ya ce, “Babu wata da ta yi kyakkyawan shiri a kan wannan annobar da ta game duniya amma dole mu yi iya bakin kokarin mu domin yakar ta, sannan kuma mu ci gaba da bunkasa abin da mu ke da shi a kasa a kowacce rana,