Ma’aikacin gona, Abdurrahman dan kauyen Goodinabali a garin Bantwal taluk ya sayawa ma su karamin karfi kayan abinci da kudin da ya tara domin zuwa aikin Hajji.
Sai da ya zo daf da cika burin sa, sai ya karke da kashe duk abin da ya tara na tsawon lokaci domin ya ciyar da marasa karfi a lokacin dokar hana fita da a ka sanya sabo da a dakile yaduwar coronavirus.
Abdurrahman ya sadaukar da rayuwar sa ne wajen kulawa da iyalin sa da kuma cika burin sa na zuwa sauke farali a kasa mai tsarki.
Amma kuma burin nasa bai cika ba sakamakon kashe kudin da ya tara wajen sayan kayan abinci ya kuma rabawa mabukata.
IHRHAUSA ta rawaito cewa Kasar Saudi Arebiya na fama da cutar coronavirus in da ko a jiya ma sama da mutane dubu daya ne suka kamu, lamarin da ya haifar da shakku a kan yiwuwar yin aikin Hajjin na bana.