Ma’ikatar Kula da Masallatan Harami Biyu ta fara saka kofofi masu na’urar kashe kwayoyin cuta a masallacin Harami.
Sabuwar na’urar za ta rika bincikawa da kashe kwayoyin cutar da ke jikin masu shigewa ta kofar kafin su shiga masallacin.
An fara gwada na’urar kashe kwayoyin cutar a kofar shiga Harami na Makka.
Daga bisani kuma sai a sassaka kofofin idan a ka tabbatar da sakamakon gwajin da a ka yi na na’urar da a ka sanya ta a kofa mai suna KING ABDUL’AZIZ.