Nan da makonni biyu alhazan Nijeriya za su san matsayin su kan Hajjin 2020

0
247

Daga Mustapha Adamu
Yayin da a ke cikin halin dar-dar da rashin tabbas a kan ko za a yi Aikin Hajjin bana ko ba za a yi ba, Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan bayyana cewa hukumar za ta fitar da matsaya a karshen watan Ramadan. 
Yayin da shugaban ya bakunci shiri mai taken “Hajj bulaguro don bauta” a hadakar gidajen rediyon tarayya ranar Juma’a, ya ce, da ya ke ba zai yiwu hukumar ta yanke hukunci a kan ko za a yi Aikin Hajjin bana ko ba za a yi ba, ya tabbatar da cewa muddin Saudiyata fitar da matsaya, to itama hukumar za ta fadi tata matsayar ba tare da bata lokaci ba. 
“Zan baku cikakkiyar amsa bayan watan Ramadan, nan da makonni biyu kenan, lokacin da mahukunta a Saudiya za su fidda matsaya cewa zai yiwu ko ba zai yiwu ba. Tabbas a na nan a na ci gaba da tattaunawa kan tsare-tsaren Hajjin bana dama komai da komai, ni kuma sai na sanar da ya’n Nijeriaya,”
Alhaji Zikrullah ya nuna yakinin cewa bude masallatai biyu masu tsarki na Maka da Madina wata manuniya ce cewa za a yi Aikin Hajjin bana. 
“Kamar abinda ya faru a ya’n kwanakin da su ka gabata na bude masallatan harami masu tsarki ga al’umma domin su ci gaba da bauta, wani mataki me da ya bamu kwarin gwiwar cewa za a yi Aikin Hajjin bana,”
Mousa Ubandawaki, Mataimakin Daraktan buge-bugen takardu da wallafe-wallafe na Hukumar, ya rawaito shugaban na cewa “Hukumar nan ba ta da hurumin ta yanke cewa ko za a yi Aikin Hajjin bana ko ba za a yi ba. Mu mun dogara ne da wasu dalilai. Misali, ko sararin samaniyar Nijeriya din ma a kulle ya ke har nan da makonni hudu ma su zuwa kuma suma Saudiya din hakan take. Ba damar tashi da saukar jirage har sai an bude sararin samaniyar.”
Sai dai kuma ya ce duk hukuncin da Saudiya ta yanke, to hukumar ba za ta yi sakaci da lafiya da walwalar alhazan Nijeriya ba.
“Ba za mu yi ganganci da rayuwar ko daya daga cikin alhazan mu ba. Duk wani mataki da za mu dauka to za mu dauka ne da zuciya daya. Ba za mu yi ganganci mu ce dole sai mun yi Aikin Hajji ko ta wanne hali ba,”
Da ya ke amsa tambayar da wani mai sauraro ya yi masa ta wayar tarho, Alhaji Zikrullah ya bayyana cewa, a kan annobar COVID-19, hukumar ta yi hadin gwiwa mai karfi da Hukumar lafiya ta kasa a kan wayarwa da alhazai kai don ganin cewa sun saba da matakan kariya kamar su zama a nesa da juna, amfani da takunkumi, da kuma tsaftar jiki ta yadda ba za su kamu da cutar ba, ba kuma za su yada ta ba. 
Ya kuma zayyana wasu fafutuka da hukumar ta ke yi wajen wayar da kan alhazai ta kafafe daban-daban kamar su wallafa kasidu da mujallu da kuma umartar Hukumomin Kula da Walwalar Alhazai na jihohi da su shiga gidajen rediyo da telebijin da kuma kafofin sadarwa na zamani domin ilimantar da maniyyata a yankin da suke. 
Shugaban ya kara jaddada kudurin hukumar na rage kudin Aikin Hajji da kuma yawan kwanakin da alhazai su ke yi a kasa mai tsarki, inda ya ce yana nan yana ta aiwatar da dabaru domin cimma wannan bukatar da za ta fara aiki tun daga Hajjin bana idan ya yiwu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here